Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Kolossiyawa 1:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Shi ne surar Allah marar ganuwa, magāji ne tun ba a halicci kome ba,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Kolossiyawa 1:15
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Shi ne hasken ɗaukakar Allah, ainihin kamannin zatinsa kuma, shi kuma yana a riƙe da dukan abubuwa ta ikon faɗarsa. Bayan da ya tsarkake zunubanmu, sai ya zauna a dama da Maɗaukaki a can Sama.


Yesu ya ce masa, “Na daɗe tare da ku haka, amma har yanzu ba ka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Nuna mana Uban’”?


Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne.


Su ne marasa ba da gaskiya, waɗanda sarkin zamanin nan ya makantar da hankalinsu, don kada hasken bisharar ɗaukakar Almasihu, shi da yake surar Allah, ya haskaka su.


Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi.


Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.


wanda, ko da yake a cikin surar Allah yake, bai mai da daidaitakar nan tasa da Allah abar da zai riƙe kankan ce ba,


Domin shi Allah wanda ya ce, “Haske yă ɓullo daga duhu ya haskaka,” shi ne ya haskaka zukatanmu domin a haskaka mutane su san ɗaukakarsa a fuskar Yesu Almasihu.


Zan maishe shi ɗan farina, Mafi girma daga cikin dukan sarakuna.


Waɗanda Allah ya riga ya zaɓa tun tuni, su ne ya ƙaddara su ɗauki kamannin Ɗansa, domin shi Ɗan yă zama na farko a cikin 'yan'uwa masu yawa.


Girma da ɗaukaka su tabbata ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, marar ganuwa, Allah Makaɗaici, har abada abadin. Amin, amin.


“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Lawudikiya haka, ‘Ga maganar tabbataccen nan, Amintaccen Mashaidi mai gaskiya, wanda ta wurinsa dukkan halittar Allah ta kasance.


Amma da zai sāke shigo da magāji a duniya, sai ya ce, “Dukkan mala'ikun Allah su yi masa sujada.”


Shi ne kaɗai marar mutuwa, yake kuma zaune a cikin hasken da ba ya kusatuwa. Shi kuwa ba mutumin da ya taɓa ganinsa, ko kuwa zai iya ganinsa. Girma da madawwamin mulki su tabbata a gare shi. Amin, amin.


Da ba domin na yi ayyuka a cikinsu da ba wanda ya taɓa yi sai ni ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gani, sun kuma ƙi mu, ni da Ubana duka.


“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.


Ya tsamo mu daga mulkin duhu, ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ɗansa,


Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, bai ji tsoron fushin sarki ba, ya kuwa jure saboda yana ganin wannan da ba ya ganuwa.


Nakan yi magana da shi fuska da fuska a sarari, ba a duhunce ba. Yakan kuma ga zatina. Me ya sa ba ku ji tsoron zargin bawana Musa ba?”


Suka ga Allah na Isra'ila. Wurin da yake ƙarƙashin tafin ƙafafunsa yana kama da daɓen da aka yi da dutsen yakutu, garau kamar sararin sama.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ