Almasihu ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak, ba ƙari, ba kuwa ta wurin jinin awaki ko na 'yan maruƙa ya shiga ba, sai dai ta wurin nasa jini, ya samo mana madawwamiyar fansa.
Suna raira sabuwar waƙa, suna cewa, “Macancanci ne kai ka ɗauki littafin nan, ka ɓamɓare hatimansa, Domin dā an kashe ka, ka kuma fanso wa Allah mutane ta jininka Daga kowace kabila, da kowane harshe, da kowace jama'a, da kowace al'umma,
Almasihu ya fanso mu daga la'anar nan ta Shari'a, da ya zama abin la'ana saboda mu, domin a rubuce yake cewa, “Duk wanda aka kafa a jikin itace, la'ananne ne.”
da kuma Yesu Almasihu Amintaccen Mashaidi, na farko a cikin masu tashi daga matattu, mai mulkin sarakunan duniya. Ɗaukaka da mulki su tabbata har abada abadin ga wanda yake ƙaunarmu, ya kuma ɓalle mana ƙangin zunubanmu ta wurin jininsa,
Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah. An kashe shi a jiki, amma an rayar da shi a ruhu.
Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.
Sai Bitrus ya ce musu, “Sai ku tuba, a yi wa ko wannenku baftisma, a kan kun yarda da sunan Yesu Almasihu, domin a gafarta zunubanku, za ku kuwa sami baiwar Ruhu Mai Tsarki,
domin ka buɗe musu ido, su juyo daga duhu zuwa haske, daga kuma mulkin Shaiɗan zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai, da kuma gādo tare da dukan tsarkaka saboda sun gaskata da ni.’ ”
Waɗannan su ne waɗanda ba su taɓa ƙazantuwa da fasikanci ba, domin su tsarkaka ne. Su ne kuma suke bin Ɗan Ragon a duk inda ya je. Su ne kuma aka fanso daga cikin mutane a kan su ne nunan fari na Allah, da na Ɗan Ragon nan kuma,
Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa.