Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 9:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Sai Musa ya ce musu, “Dakata, har na ji abin da Ubangiji zai umarta a kanku.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Musa ya amsa musu ya ce, “Ku dakata sai na sami umarni daga wurin Ubangiji game da ku.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 9:8
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ina kasa kunne ga abin da Ubangiji Allah yake cewa, Mu da muke mutanensa, ya alkawarta mana salama, Idan ba mu koma kan al'amuranmu na wauta ba.


Abin nan kuwa da na karɓa a gun Ubangiji, shi ne na ba ku, cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki gurasa,


Ban sani ina da wani laifi ba, amma ba don wannan na kuɓuta ba, ai, Ubangiji shi ne mai gwada ni.


domin ban ji nauyin sanar da ku dukan nufin Allah ba.


Domin kuwa maganar da ka faɗa mini na faɗa musu, sun kuwa karɓa, sun kuma san hakika na fito daga wurinka ne, sun kuma gaskata kai ne ka aiko ni.


Duk mai son aikata nufin Allah zai san koyarwan nan ko ta Allah ce, ko domin kaina nake faɗa.


“Ɗan mutum, na maishe ka mai tsaron gidan Isra'ila. Sa'ad da ka ji magana daga bakina, sai ka faɗakar da su a madadina.


Za ka faɗa musu maganata, ko su ji, ko kada su ji, gama su 'yan tawaye ne.


Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi, Yakan koya musu alkawarinsa.


Ba ku za ku yi wannan yaƙi ba, ku dai, ku jā dāga, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ciwo muku, ya Yahuza da Urushalima. Kada ku ji tsoro ko ku razana, gobe ku fita ku tsaya gāba da su, gama Ubangiji yana tare da ku.’ ”


Sai Musa ya ce wa jama'a, “Kada ku tsorata, ku tsaya cik, ku ga ceton Ubangiji, wanda zai yi muku yau, gama Masarawan nan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba faufau.


Sai Musa ya ce wa surukinsa, “Mutane suna zuwa wurina ne domin su san faɗar Allah.


suka ce masa, “Ai, mun ƙazantu saboda mun taɓa gawa. Me ya sa aka hana mu mu ba da hadaya ga Ubangiji tare da sauran 'yan'uwanmu a ƙayyadadden lokacin yinta?”


Aka sa shi a gidan waƙafi domin ba a bayyana abin da za a yi da shi ba tukuna.


Musa kuwa ya kulle shi a gidan tsaro kafin Ubangiji ya faɗa musu abin da za su yi da shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ