4 Musa kuwa ya faɗa wa Isra'ilawa su kiyaye Idin Ƙetarewa.
4 Saboda haka sai Musa ya gaya wa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa,
Musa ya kirayi dattawan Isra'ila duka, ya ce musu, “Gaggauta, ku zaɓa wa kanku ɗan tunkiya ko akuya bisa ga iyalanku, ku yanka domin Idin Ƙetarewa.
A rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, da maraice za su kiyaye shi a ƙayyadadden lokacinsa bisa ga dokokinsa da ka'idodinsa duka.”
Sai suka kiyaye Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan farko da maraice a cikin jejin Sinai bisa ga dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. Haka kuwa Isra'ilawa suka yi.