2 “Sai Isra'ilawa su kiyaye Idin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokacinsa.
2 “Ka sa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokaci.
Yosiya kuwa ya yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji a Urushalima. A rana ta goma sha huɗu ga wata na fari suka yanka ragon Idin Ƙetarewa.
Da maraice a rana ta goma sha huɗu ga watan fari, ita ce ranar Idin Ƙetarewa ta Ubangiji.
Sai ranar idin abinci marar yisti ta zo, wato, rana da ake yanka ɗan ragon Idin Ƙetarewa.
A ranar farko ta idin abinci marar yisti, wato ran da aka saba yanka ɗan ragon Idin Ƙetarewa, sai almajiransa suka ce masa, “Ina kake so mu je mu shirya maka cin Idin Ƙetarewa?”
A rana ta goma sha huɗu ga watan fari, sai waɗanda suka komo daga bauta suka kiyaye Idin Ƙetarewa.
Sa'ad da Isra'ilawa suke zaune a Gilgal, sai suka yi Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan, da maraice, a filayen Yariko.
Za a yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji a rana ta goma sha huɗu ga watan fari.
A rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, da maraice za su kiyaye shi a ƙayyadadden lokacinsa bisa ga dokokinsa da ka'idodinsa duka.”
Sarki Yosiya kuwa ya umarci dukan mutane, ya ce, “Ku kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku kamar yadda aka rubuta a littafin alkawari.”