Ya ku ƙaunatattu, tun da aka yi mana waɗannan alkawarai, sai mu tsarkake kanmu daga kowace irin ƙazanta ta jiki ko ta zuci, da bangirma ga Allah mu kamalta a cikin tsarki.
Ku fita, ku bar Babila Ku dukanku da kuke ɗauke da keɓaɓɓen kayan Ubangiji! Kada ku taɓa abin da aka hana, Ku kiyaye kanku da tsarki, Ku fita ku bar birnin.
A wannan lokaci ne Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, su kuma tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yi masa aiki, su kuma sa albarka da sunan Ubangiji kamar yadda yake a yau.
Zai zo ya yi hukunci kamar wanda yake tace azurfa, ya tsarkake ta. Zai tsarkake firistoci, ya tace su kamar yadda ake yi wa azurfa da zinariya. A sa'an nan ne za su kawo wa Ubangiji hadayun da suka dace.