Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 8:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka wanke tufafinsu. Haruna kuwa ya keɓe su, suka zama kamar hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji, ya kuma yi kafara dominsu don ya tsarkake su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma wanke tufafinsu. Sai Haruna ya miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa a gaban Ubangiji, ya kuma yi kafara saboda su don yă tsarkake su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 8:21
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ga yadda za ka tsarkake su. Ka yayyafa musu ruwan tsarkakewa. Su aske jikunansu duka, su kuma a wanke tufafinsu, sa'an nan za su tsarkaka.


A kan rana ta uku da ta bakwai kuma, wanda yake da tsarki zai yayyafa wa marar tsarkin ruwa, ya tsarkake shi. Sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, da maraice kuwa zai tsarkaka.


Bayan da ka tsarkake su, ka miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa, za su cancanta su yi aiki a alfarwa ta sujada.


A rana ta uku da ta bakwai zai tsarkake kansa da ruwa, zai kuwa tsarkaka, amma in a rana ta uku da ta bakwai bai tsarkake kansa ba, to, ba zai tsarkaka ba.


“Ga shi, na ɗauki Lawiyawa daga cikin Isra'ilawa a maimakon kowane ɗan farin da ya buɗe mahaifa daga cikin mutanen Isra'ila. Lawiyawa za su zama nawa.


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je ka wurin jama'a ka tsarkake su yau da kuma gobe, su kuma wanke tufafinsu.


Musa da Haruna kuwa da dukan taron Isra'ilawa suka yi wa Lawiyawa yadda Ubangiji ya umarce Musa, haka kuwa Isra'ilawa suka yi musu.


Bayan haka Lawiyawa suka shiga alfarwa ta sujada don su yi aiki a gaban Haruna da 'ya'yansa maza, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa a kan Lawiyawa, haka kuwa suka yi musu.


Firist ɗin da zai tsarkake mutumin zai kawo wanda za a tsarkake da waɗannan abubuwa a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ