Daga cikin Isra'ilawa kuwa na ba da Lawiyawa ga Haruna da 'ya'yansa maza don su yi wa Isra'ilawa hidima a alfarwa ta sujada, su kuma yi kafara dominsu don kada annoba ta sami Isra'ilawa sa'ad da suka kusaci alfarwa ta sujada.”
Isra'ila ya miƙa hannunsa na dama, ya ɗora bisa kan Ifraimu wanda yake ƙarami, hannunsa na hagu kuma bisa kan Manassa, yana harɗe da hannuwansa, gama Manassa shi ne ɗan fari.