“Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce, za su zama mutanena na ainihi, a ranar da na aikata. Zan ji ƙansu kamar yadda mahaifi yakan ji ƙan ɗansa wanda suke masa hidima.
Ga shi, ni na ɗauki 'yan'uwanku, Lawiyawa, daga cikin mutanen Isra'ila. Kyauta suke a gare ku, waɗanda aka bayar ga Ubangiji don su lura da alfarwa ta sujada.
“Ka keɓe Lawiyawa a maimakon dukan 'ya'yan fari na Isra'ilawa. Dabbobin Lawiyawa kuma za su zama a maimakon 'ya'yan farin dabbobin Isra'ilawa. Lawiyawa kuwa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.
A wannan lokaci ne Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, su kuma tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yi masa aiki, su kuma sa albarka da sunan Ubangiji kamar yadda yake a yau.