suka kawo hadayarsu a gaban Ubangiji, karusai shida rufaffu, da takarkarai goma sha biyu. Shugabanni biyu suka ba da karusa ɗaya, kowannensu kuwa ya ba da takarkari ɗaya, da suka gama miƙa su,
Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah daga gidan Abinadab, wanda yake bisa tudu. Suka sa akwatin alkawari a sabuwar karusa. Uzza da Ahiyo, 'ya'yan Abinadeb, maza, suka bi da karusar da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo ne yake tafiya a gaban akwatin alkawarin.