Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 7:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Bari shugabannin su kawo hadayunsa domin keɓewar bagade, har kwana sha biyu, kowa a ranarsa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa cewa, “Kowace rana, shugaba guda zai kawo hadayarsa saboda keɓewar bagade.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 7:11
5 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Don ko da yake a jiki ba na nan, ai, ruhuna yana nan tare da ku, ina kuwa farin cikin ganin kyakkyawan tsarinku, da dagewarku a kan bangaskiyarku ga Almasihu.


Sai dai a yi kome ta hanyar da ta dace, a shirye kuma.


domin Allah ba Allahn ruɗu ba ne, na salama ne. Haka yake kuwa a duk ikilisyoyin tsarkaka.


Sai shugabanni suka miƙa hadayu domin keɓewar bagade a ranar da aka zuba masa mai. Suka fara miƙa sadakokinsu a bagaden,


Suka miƙa hadayunsu bi da bi kamar haka, Rana Kabila Shugaba Rana ta farko Yahuza Nashon ɗan Amminadab Rana ta biyu Issaka Netanel ɗan Zuwar Rana ta uku Zabaluna Eliyab ɗan Helon Rana ta huɗu Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur Rana ta biyar Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai Rana ta shida Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel Rana ta bakwai Ifraimu Elishama ɗan Ammihud Rana ta takwas Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur Rana ta tara Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni Rana ta goma Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai Rana ta goma sha ɗaya Ashiru Fagiyel ɗan Okran Rana ta goma sha biyu Naftali Ahira ɗan Enan Hadayun da kowannensu ya kawo duk daidai da juna suke, farantin azurfa na shekel ɗari da talatin, da kwanon azurfa na shekel saba'in, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi, duka suna cike da garin da aka kwaɓa da mai domin hadaya ta gari, cokali na zinariya guda na shekel goma, cike da kayan ƙanshi, da ɗan bijimi guda, da rago ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya domin hadaya ta ƙonawa, da akuya guda domin hadaya ta zunubi, da bijimai biyu, da raguna biyar, da awaki biyar, da 'yan raguna biyar bana ɗaya ɗaya, domin hadaya ta salama.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ