Ƙidaya 7:10 - Littafi Mai Tsarki10 Sai shugabanni suka miƙa hadayu domin keɓewar bagade a ranar da aka zuba masa mai. Suka fara miƙa sadakokinsu a bagaden, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Sa’ad da aka shafe bagaden da mai, sai shugabannin suka kawo hadayunsu saboda keɓewarsa, suka miƙa su a bagaden. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga jimillar hadayun da shugabanni goma sha biyu suka kawo domin keɓewar bagaden: farantan azurfa goma sha biyu da kwanonin azurfa goma sha biyu, duka nauyinsu shekel dubu biyu da ɗari huɗu cokulan zinariya goma sha biyu, nauyinsu duka shekel ɗari da ashirin cike da kayan ƙanshi bijimai goma sha biyu, da raguna goma sha biyu, da 'yan raguna goma sha biyu bana ɗaya ɗaya, da kuma hadaya ta gari da za a haɗa da waɗannan domin hadaya ta ƙonawa awaki goma sha biyu domin hadaya don zunubi bijimai ashirin da huɗu, da raguna sittin, da awaki sittin, da 'yan raguna bana ɗaya ɗaya guda sittin domin hadaya ta salama.