Allah mai kawo sa zuciya, yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama saboda bangaskiyarku, domin ku yi matuƙar sa zuciya ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
Bayan kwana takwas har wa yau almajiransa na cikin gidan, Toma ma yana nan tare da su, ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce, “Salama alaikun.”
Zai zama salamarmu. Sa'ad da kuma Assuriyawa za su kawo mana yaƙi, Za su tattake kagaranmu, Za mu sa makiyaya bakwai da shugabanni takwas su yi gāba da su.
Ba da takubansu suka ci ƙasar ba, Ba kuwa da ikonsu suka rinjayi ƙasar ba, Amma da ikonka ne da kuma ƙarfinka, Ta wurin tabbatar musu kana tare da su, Kana nuna musu kana ƙaunarsu.