Sai Ubangiji ya ce masa, “Zan wuce a gabanka, Ni Ubangiji zan yi shelar sunana a gabanka, zan kuma yi alheri ga wanda nā yi wa alheri, in nuna jinƙai ga wanda nā yi wa jinƙai.”
Sai ya ɗaga idanunsa, ya ga ɗan'uwansa Biliyaminu, ɗan da mahaifiyarsa ta haifa, ya ce, “Wannan shi ne auta naku, wanda kuka yi mini magana a kansa? Allah ya yi maka alheri ɗana!”
Daga Bulus zuwa ga dukan ƙaunatattun Allah da kuke a Roma, tsarkaka kirayayyu. Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.