Allah kansa, mai zartar da salama, yă tsarkake ku sarai, ya kuma kiyaye ruhunku da ranku da jikinku ƙalau, ku kasance marasa abin zargi a ranar komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
“Ni Ubangiji, na kira ka, na kuma ba ka iko Domin ka ga ana aikata gaskiya a duniya. Ta wurinka zan yi wa dukan mutane alkawari, Ta wurinka zan kawo haske ga al'ummai.
Yanzu kuma ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai tsarki, ka kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni, su zama ɗaya kamar yadda muke.
Ga shi, ina tare da kai, zan kiyaye ka duk inda ka tafi, zan kuwa komo da kai ƙasan nan, gama ba zan rabu da kai ba, sai na aikata abin nan da na hurta maka.”
Ka yarda da farin ciki ka sa wa gidan bawanka albarka domin gidansa ya dawwama a gabanka har abada, gama kai ne ka faɗa, ya Ubangiji Allah. Ka sa albarkarka ta tabbata a gidan bawanka har abada.”