Sai Haruna ya ta da hannuwansa wajen jama'a, ya sa musu albarka sa'an nan ya sauka daga wurin yin hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa, da hadayun salama.
Wannan ita ce ka'ida a kan keɓaɓɓe wanda ya ɗau wa'adi. Hadayarsa ga Ubangiji za ta zama bisa ga keɓewarsa, banda kuma abin da ya iya bayarwa. Sai ya cika wa'adin da ya ɗauka bisa ga ka'idar keɓewarsa.
Sa'an nan sai firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, su fito gaba, gama su ne Ubangiji Allahnku ya zaɓa don su yi masa aiki, su sa albarka da sunansa, su ne kuma masu daidaita kowace gardama da cin mutunci.