Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 5:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Dukan sadakoki na tsarkakakkun abubuwa na Isra'ilawa waɗanda sukan kawo wa firist, za su zama nasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Dukan tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka kawo wa firist za su zama nasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 5:9
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Duk hadayu na ɗagawa na tsarkakakkun abubuwan da Isra'ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da 'ya'yanka mata da maza a kowane lokaci. Wannan alkawarin gishiri ne na Ubangiji dominka da zuriyarka.”


Wannan zai zama rabon Haruna da na 'ya'yansa maza daga wurin Isra'ilawa. Gama wannan hadaya ta ɗagawa ce daga cikin hadayu na salama da Isra'ilawa za su miƙa wa Ubangiji.


Za ku ci shi a wuri mai tsarki gama naka rabo ke nan da na 'ya'yanka maza daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji, gama haka Ubangiji ya umarce ni.


Firist wanda ya miƙa hadaya don zunubi zai ci daga ciki a wuri mai tsarki a cikin farfajiyar alfarwa ta sujada.


Za a ba firist cinya ta dama, don hadaya ta ɗagawa daga cikin hadayu na salama.


Gama Ubangiji ya ba Haruna da 'ya'yansa maza, ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka ɗaga, su zama rabonsu daga cikin hadayu na salama na Isra'ilawa. Ya ba Haruna, firist, da 'ya'yansa maza, su zama rabonsu har abada daga cikin hadayu na Isra'ilawa.


Amma ƙirjin da aka yi hadayar ta kaɗawa da shi da cinyar da aka miƙa, za ka ci su a kowane tsabtataccen wuri, da kai da 'ya'yanka mata da maza, gama wannan ne rabon da aka ba ku, daga hadayun salama na Isra'ilwa.


Za su kawo cinyar hadayar ɗagawa da ƙirjin hadayar kaɗawa tare da kitsen hadayun ƙonawa domin a yi hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. Wannan zai zama rabonka da na 'ya'yanka har abada kamar yadda Ubangiji ya umarta.”


Idan wanda ya yi wa laifin ya rasu, ba shi kuma da wani dangi na kusa wanda za a ba diyyar, sai a kai diyyar gaban Ubangiji domin firist, tare da ragon hadaya, don yin kafarar da za a yi masa.


Sai Musa ya ba Ele'azara firist rabon Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.


Amma tsarkakakkun abubuwan da suke wajibanku da hadayunku na wa'adi, su ne za ku ɗauka ku kai wurin da Ubangiji ya zaɓa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ