Idan sadakarsa ta hadayar ƙonawa ce daga cikin garken shanu, sai ya ba da namiji marar lahani, zai miƙa shi a ƙofar alfarwa ta sujada domin sadakar ta zama abar karɓa a gaban Ubangiji.
duk da haka sai mutum ya kawo matarsa a gaban firist, ya kawo kuma hadayar da ake bukata, wato humushin garwar garin sha'ir, amma kada ya zuba mai ko kayan ƙanshi, gama hadaya ce domin kishi, domin a bayyana gaskiya a fili.