Ƙidaya 4:49 - Littafi Mai Tsarki49 Aka ba kowannensu aikinsa da ɗaukar kaya bisa ga umarnin da Ubangiji ya yi wa Musa. Haka kuwa aka ƙidaya su kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202049 Bisa ga umarnin Ubangiji ta wurin Musa, aka ba kowa aikinsa, aka kuma faɗa musu abin da za su ɗauka. Ta haka aka ƙidaya su, yadda Ubangiji ya umarci Musa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da Haruna da 'ya'yansa maza suka gama kintsa Wuri Mai Tsarki da kayayyakinsa duka a lokacin tashi, sai 'ya'yan Kohat, maza, su zo su ɗauke kayayyakin, amma kada su taɓa abubuwan nan masu tsarki domin kada su mutu. Waɗannan su ne ayyukan 'ya'yan Kohat a duk lokacin da za a naɗe alfarwa ta sujada.