Ƙidaya 4:33 - Littafi Mai Tsarki33 Wannan shi ne aikin iyalan 'ya'yan Merari, maza. Aikinsu ke nan duka a alfarwa ta sujada. Itamar ɗan Haruna, firist, shi ne zai shugabance su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202033 Wannan ce hidimar da mutanen Merari za su yi a aikin Tentin Sujada, a ƙarƙashin jagorancin Itamar ɗan Haruna, firist.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Musa da Haruna da shugabannin taron jama'a kuwa suka ƙidaya iyalan Lawiyawa uku, wato Kohatawa, da Gershonawa da Merariyawa bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu, aka rubuta dukan mazaje daga mai shekara talatin zuwa mai shekara hamsin, waɗanda za su iya aiki a alfarwa ta sujada, kamar haka, Kohat dubu biyu da ɗari bakwai da hamsin (2,750), Gershon dubu biyu da ɗari shida da talatin (2,630), Merari dubu uku da ɗari biyu (3,200), Jimilla duka, dubu takwas da ɗari biyar da tamanin (8,580).