29 Ubangiji kuma ya faɗa wa Musa ya ƙidaya Merariyawa bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu,
29 “Ka ƙidaya kabilar Merari bisa ga kabilarsu da iyalansu.
Wannan shi ne aikin da iyalan Gershonawa za su yi a alfarwa ta sujada. Itamar ɗan Haruna, firist, shi zai shugabance su cikin aikin da za su yi.
ya rubuta su tun daga mai shekara talatin, har zuwa mai shekara hamsin, duk wanda ya isa yin aikin da zai yi a alfarwa ta sujada.
da kuma dirkoki na farfajiyar da ta kewaye wurin, da kwasfa da turaku da igiyoyinsu.
Ya kuwa ba 'ya'ya maza na Merari karusai huɗu da takarkarai takwas bisa ga aikinsu, a hannun Itamar ɗan Haruna, firist.