“Dukan matanka da 'ya'yanka za a kai su wurin Kaldiyawa, kai kanka kuma ba za ka tsere musu ba, amma Sarkin Babila zai kama ka, birnin kuma za a ƙone shi da wuta.”
Sai Ubangiji ya kashe mutum saba'in daga cikin mutanen Bet-shemesh domin sun leƙa cikin akwatin alkawari na Ubangiji. Mutanen kuwa suka yi makoki ƙwarai domin Ubangiji ya kashe mutane da yawa daga cikinsu.
ta hallaka ta wurin kusatar waɗannan tsarkakakkun abubuwa. Maganin abin, shi ne sai Haruna da 'ya'yansa maza, su shiga, su nuna wa kowannensu irin aikin da zai yi, da kayan da zai ɗauka.