Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 4:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Ele'azara kuwa, ɗan Haruna, firist, shi ne zai lura da man fitila, da turare, da hadayar gari ta kullum, da man keɓewa, ya kuma kula da dukan alfarwar, da duk abin da yake cikinta, da Wuri Mai Tsarki, da kayayyakinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 “Eleyazar ɗan Haruna firist zai lura da man fitila da turare da hadaya ta gari na kullum da kuma keɓaɓɓen mai. Shi ne zai lura da dukan tabanakul da duk abin da yake cikinsa da kuma kayayyaki da abubuwan masu tsarki.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 4:16
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

da mai domin fitila, da kayan yaji domin man keɓewa, da turaren ƙonawa,


ya umarce Isra'ilawa, su kawo masa tsabtataccen man zaitun da aka matse domin fitilar. Fitilar za ta riƙa ci kullum.


A dā kun ɓăce kamar tumaki, amma a yanzu kun dawo ga Makiyayi, wato mai kula da rayukanku.


ku yi kiwon garken Allah da yake tare da ku, ba a kan tilas ba, sai dai a kan yarda, ba ma don neman ribar banza ba, sai dai da himma.


amma Almasihu mai aminci ne, yana mulkin jama'ar Allah a kan shi Ɗa ne, mu ne kuwa jama'arsa, muddin mun tsaya gabanmu gaɗi, muna gadara da begenmu ƙwarai.


Saboda haka, ya ku 'yan'uwa tsarkaka, ku da kuke da rabo a kiran nan basamaniya, sai ku tsai da zuciya ga Yesu, Manzo, da kuma Babban Firist na bangaskiyar da muke shaidawa,


Domin Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya ne, a tsakanin Allah da mutane, Almasihu Yesu, mutum,


Ta haka ya kamata a san mu da zama ma'aikatan Almasihu, masu riƙon amanar asirtattun al'amuran Allah.


Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.


“Ruhun Ubangiji yana tare da ni, Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara. Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru, In kuma buɗe wa makafi ido, In kuma 'yanta waɗanda suke a danne,


Ele'azara, ɗan Haruna, firist, shi zai shugabanci shugabannin Lawiyawa, shi ne kuma zai lura da waɗanda suke aiki a Wuri Mai Tsarki.


domin keɓe firist, wato, zuriyar Haruna. A ranar da za a keɓe shi zai kawo humushin garwar gari mai laushi (kamar yadda akan kawo na hadaya ta gari), za a miƙa rabinsa da safe, rabin kuma da maraice.


Ya yi tsattsarkan mai na keɓewa da kuma turare mai ƙanshi yadda mai yin turare yakan yi.


da man keɓewa, da turaren nan mai ƙanshi domin Wuri Mai Tsarki. Za su yi su duka kamar yadda na umarce ka.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ