Ƙidaya 4:15 - Littafi Mai Tsarki15 Sa'ad da Haruna da 'ya'yansa maza suka gama kintsa Wuri Mai Tsarki da kayayyakinsa duka a lokacin tashi, sai 'ya'yan Kohat, maza, su zo su ɗauke kayayyakin, amma kada su taɓa abubuwan nan masu tsarki domin kada su mutu. Waɗannan su ne ayyukan 'ya'yan Kohat a duk lokacin da za a naɗe alfarwa ta sujada. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202015 “Bayan Haruna da ’ya’yansa suka gama rufe kayayyaki masu tsarki da dukan abubuwa masu tsarki, sa’ad da kuma aka shirya tashi daga sansani, sai Kohatawa su zo gaba, su ɗauka. Amma kada su taɓa abubuwa masu tsarki, don kada su mutu. Kohatawa za su ɗauki abubuwan da suke cikin Tentin Sujada. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |