Ƙidaya 4:12 - Littafi Mai Tsarki12 Su ɗauki dukan kwanonin da ake amfani da su a Wuri Mai Tsarki, su sa su cikin shuɗin zane, sa'an nan su rufe su da fatun awaki, a sarƙafa su a sanda don a ɗauka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 “Za su ɗauki dukan kayayyakin da ake amfani da su a wuri mai tsarki, su nannaɗe su da zane mai ruwan shuɗi, su rufe shi da fatar shanun teku, sa’an nan a sa su a kan sandan ɗaukarsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Haka kuwa Sulemanu ya yi dukan kayayyakin nan da suke cikin Haikalin Allah, duk da zinariya tsantsa aka yi su. bagade na zinariya tebur don ajiye gurasar ajiyewa alkukai tare da fitilunsu na zinariya tsantsa, domin a kunna su a gaban Wuri Mafi Tsarki na ciki kamar yadda aka tsara furanni fitilu arautaki hantsuka daruna cokula farantan wuta ƙofofi na can ciki ƙofofi na waje.
Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da daruna. Huram kuwa ya gama dukan aikin da ya alkawarta wa sarki Sulemanu a Haikalin Allah: ginshiƙi biyu dajiya biyu a kan ginshiƙi biyu siffar tukakkiyar sarƙa a kan kowane ginshiƙi Siffar rumman guda ɗari huɗu domin raga don rufe dajiyar ginshiƙan dakali goma daro goma kwatarniya. Bijimi goma sha biyu da suke ɗauke da kwatarniya kwanoni, manyan cokula masu yatsotsi, wato ya yi dukan kayan nan da tagulla domin Haikalin Ubangiji.