11 Suka auri 'ya'yan 'yan'uwan mahaifinsu.
11 ’Ya’yan Zelofehad mata, Mala, Tirza, Hogla, Milka da Nowa, suka auri ’ya’yan ’yan’uwa na gefen mahaifinsu.
Sai 'ya'yan Zelofehad, mata, ɗan Hefer ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manassa, ɗan Yusufu, suka tafi ƙofar alfarwa ta sujada. Sunayen 'ya'ya, matan ke nan, Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.
Zelofehad, ɗan Hefer, ba shi da 'ya'ya maza, sai dai 'ya'ya mata. Sunayen 'ya'yansa mata su ne Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.
Sai 'ya'yan Zelofehad mata, wato Mala, da Tirza, da Hogla, da Milka, da Nowa suka yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Sun yi aure a cikin iyalan 'ya'yan Manassa, ɗan Yusufu. Gādonsu kuwa bai ɓalle daga cikin kabilar iyalin kakansu ba.