Isra'ilawa za su ba Lawiyawa biranen nan bisa ga girman mallakarsu. Manyan kabilai za su ba su birane da yawa, amma ƙananan kabilai za su ba su birane kaɗan.”
Wannan shi ne tanadi domin wanda ya yi kisankai, wato wanda zai gudu zuwa can don ya tsira. Idan ya kashe abokinsa ba da niyya ba, ba kuma ƙiyayya a tsakaninsu a dā,