Ya kafa iyakar Isra'ila daga ƙofar Hamat har zuwa tekun Araba. Wannan kuwa shi ne abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya faɗa ta bakin bawansa annabi Yunana, ɗan amittai, daga Gathefer.
Amma sojojin Kaldiyawa suka bi su, suka ci wa Zadakiya a filayen Yariko. Suka kama shi, suka kawo shi gaban Sarkin Babila a Ribla a ƙasar Hamat, a can Nebukadnezzar ya yanka masa hukunci.
Sa'an nan kuma Sulemanu ya yi biki na kwana bakwai, shi da dukan jama'ar Isra'ila. Mutane suka zo, tun daga Mashigin Hamat a arewa, har zuwa iyakar ƙasar Masar a kudu, suka hallara a gaban Ubangiji Allahnmu.
Ubangiji Allah Mai Runduna kansa, ya amsa ya ce, “Zan aiko da wata al'umma ta yi gāba da ku, ya Isra'ilawa. Za ta matse muku Tun daga mashigin Hamat wajen arewa, Har zuwa Kwarin Urdun a kudu.”
Haka fa, Dawuda ya tattara dukan Isra'ilawa wuri ɗaya, daga Shihor ta Masar, har zuwa mashigin Hamat domin a kawo akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim.