Iyakar ƙasarsu daga wajen kudu ta miƙa tun daga wajen jejin Zin, har zuwa iyakar Edom. Iyakarsu kuwa ta wajen kudu za ta fara daga ƙarshen Tekun Gishiri wajen gabas.
Ubangiji Allah Mai Runduna kansa, ya amsa ya ce, “Zan aiko da wata al'umma ta yi gāba da ku, ya Isra'ilawa. Za ta matse muku Tun daga mashigin Hamat wajen arewa, Har zuwa Kwarin Urdun a kudu.”