A wannan rana Ubangiji ya yi wa Abram alkawari ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga Kogin Masar zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis ke nan,
A wannan rana Ubangiji kansa zai hukunta jama'arsa, Isra'ila, daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, tun daga Yufiretis har zuwa iyakar Masar. Zai raba tsakanin nagari da mugu.
Sa'an nan kuma Sulemanu ya yi biki na kwana bakwai, shi da dukan jama'ar Isra'ila. Mutane suka zo, tun daga Mashigin Hamat a arewa, har zuwa iyakar ƙasar Masar a kudu, suka hallara a gaban Ubangiji Allahnmu.