Ga Biliyaminu mafi ƙanƙanta Cikin kabilai, a kan gaba, Sa'an nan shugabannin Yahuza da ƙungiyarsu, Daga nan sai shugabannin Zabaluna da na Naftali suna biye da su.
A kan Biliyaminu, ya ce, “Shi ƙaunatacce na Ubangiji ne, Yana zaune lafiya kusa da shi, Ubangiji yana yi masa garkuwa dukan yini, Yana zaune a kan kafaɗunsa.”