Gama Ubangiji ya riga ya yi magana a kansu, cewa lalle za su mutu a jeji. Ba wani mutumin da ya ragu daga cikinsu, sai dai Kalibu ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun.
Har yanzu kuwa ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta raɗa masa suna Yahuza. Daga nan sai ta daina haihuwa.
A lokacin da Isra'ila yake zaune a ƙasar, Ra'ubainu ya je ya kwana da Bilha kwarkwarar mahaifinsa, Isra'ila kuwa ya sami labari. 'Ya'yan Isra'ila, maza, su goma sha biyu ne.