10 Iyakarsu a wajen gabas za ta tashi tun daga Haza-enan har zuwa Shefam.
10 “ ‘Iyakarku a gabashi, za tă tashi daga Hazar-Enan zuwa Shefam.
Iyakar za ta miƙa har zuwa Zifron, ta tsaya a Hazar-enan, wannan ita ce iyakarsu a wajen arewa.
Sa'an nan za ta gangara daga Shefam zuwa Ribla wajen gabashin Ayin. Za ta kuma gangara har ta kai Tekun Galili a wajen gabas.
Iyakarsu wajen gabas ta kama daga Tekun Gishiri zuwa bakin Urdun. Wajen arewa kuwa ta miƙa daga bakin teku a inda Kogin Urdun ya gangara a tekun.
“A wajen gabas, iyakar za ta kama daga Hazar-enan tsakanin Hauran da Dimashƙu, ta bi ta Urdun tsakanin Gileyad da ƙasar Isra'ila zuwa tekun gabas har zuwa Tamar. Wannan ita ce iyakar a wajen gabas.