A wannan rana Ubangiji ya yi wa Abram alkawari ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga Kogin Masar zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis ke nan,
Suka ce, “Mu bayinka, 'yan'uwan juna ne, mu goma sha biyu muke maza, 'ya'yan mutum guda a ƙasar Kan'ana, ga shi kuwa autanmu yana tare da mahaifinmu a yanzu, ɗayan kuwa ya rasu.”
Ya tsaya, ya auna duniya, Ya duba, sai ya girgiza al'umman duniya. Sa'an nan madawwaman duwatsu suka farfashe, Madawwaman tuddai kuma suka zama bai ɗaya. Haka hanyoyinsa suke tun adun adun.