Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 33:55 - Littafi Mai Tsarki

55 Amma idan ba ku kori mazaunan ƙasar daga gabanku ba, to, waɗannan da kuka bari cikinta za su zama haki a idanunku, da ƙayayuwa a kwiyaɓunku. Za su yi ta wahalshe ku da yaƙi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

55 “ ‘Amma in ba ku kori mazaunan ƙasar ba, waɗanda kuka bari su ci gaba da zama, za su zama muku hakki a idanunku, da kuma ƙayayyuwa a bayanku. Za su ba ku wahala a ƙasar da kuke zama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 33:55
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Don haka na ce, ‘Ba zan kore muku su ba, amma za su zamar muku ƙaya, gumakansu kuwa za su zamar muku tarko.’ ”


Sai ku hallaka dukan mutanen da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku. Kada ku ji tausayinsu. Kada kuma ku bauta wa gumakansu, don kada su zamar muku tarko.


Gama za su sa 'ya'yanku su bar bina, su bauta wa gumaka. Wannan zai sa Ubangiji ya husata, ya hallaka ku da sauri.


Kada su zauna cikin ƙasarku domin kada su sa ku ku yi mini zunubi, ku bauta wa allolinsu, har abin kuwa ya zamar muku tarko.”


“ ‘A kan mutanen Isra'ila kuwa, al'ummai da suke kewaye da su, waɗanda suka raina su, ba za su ƙara zamar musu kamar sarƙaƙƙiya da ƙaya ba. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allah.’


Don kada kaina yă kumbura kuma saboda mafifitan wahayan da aka yi mini, sai aka saka mini wata cuta, wadda ta zama mini ƙaya, jakadan Shaiɗan, don yă riƙa wahalshe ni, don kada kaina ya kumbura.


Idan ba ku kore su ba, zan lalatar daku kamar yadda na shirya lalatar da su.”


domin kada ku yi cuɗanya da sauran al'umman da take zaune tare da ku, kada ku ambaci sunayen gumakansu, ko ku rantse da su, ko ku bauta musu, ko ku sunkuya musu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ