A sa'ad da Isra'ilawa duka suna tafiya a kan sandararriyar ƙasa a cikin Urdun, firistoci kuwa waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka yi ta tsayawa a bisa sandararriyar ƙasa a tsakiyar Urdun har al'ummar ta gama hayewa.
“Ku ji, ya Isra'ilawa, yau kuna kan haye Kogin Urdun, don ku kori al'ummai waɗanda suka fi ku yawa, sun kuwa fi ku ƙarfi. Suna da manyan birane masu dogon garu.
“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da kuke shiga ku mallake ta, zai korar muku da al'ummai da yawa, su Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, al'umma bakwai ke nan, waɗanda suka fi ku yawa, da kuma ƙarfi.