domin ba ku yi biyayya da umarnina ba a jejin Zin. Lokacin da dukan jama'a suka yi mini gunaguni a Meriba, ba ku nuna ikona mai tsarki a gabansu ba.” (Wannan shi ne ruwan Meriba na Kadesh a jejin Zin.)
Gama ba ku amince da ni ba a gaban mutanen Isra'ila a wurin ruwan Meriba ta Kadesh a jejin Zin a wannan lokaci, domin ba ku nuna tsarkina a gaban jama'ar Isra'ila ba.
Suka zo wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama'ar Isra'ila a jejin Faran a Kadesh. Suka faɗa musu labarin tafiyarsu, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar da suka kawo.