35 Da suka tashi daga Abrona, sai suka sauka a Eziyon-geber.
35 Suka tashi daga Abrona, suka yi sansani a Eziyon Geber.
“Muka yi gaba, muka bar zuriyar Isuwa 'yan'uwan nan namu waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai ta Seyir, muka bar hanyar Araba, da hanyar Elat da Eziyon-geber. Muka juya, muka nufi wajen jejin Mowab.
Yehoshafat ya yi jiragen ruwa a Tarshish don su tafi Ofir su kwaso zinariya, amma jiragen ba su tafi ba, gama jiragen sun farfashe a Eziyon-geber.
Sarki Sulemanu kuma ya yi jiragen ruwa a Eziyon-geber wadda take kusa da Elat, a bakin Bahar Maliya a ƙasar Edom.
Ya haɗa kai da shi, suka gina jiragen ruwa don su riƙa zuwa Tarshish. A Eziyon-geber suka gina jiragen ruwan.
Yanzu fa, tun da yake Amalekawa da Kan'aniyawa suna zaune a kwarin, gobe sai ku juya ku nufi wajen jejin ta hanyar Bahar Maliya.”
Suka kama hanya daga Yotbata suka sauka a Abrona.
Suka tashi daga Eziyon-geber suka sauka a jejin Zin, wato Kadesh.