Sai Musa ya tuɓe wa Haruna rigunansa na firist ya sa wa Ele'azara ɗan Haruna. Haruna kuwa ya rasu a kan dutsen. Sa'an nan Musa da Ele'azara suka sauko daga kan dutsen.
Za ka rasu a kan dutsen da za ka hau, za a kai ka wurin mutanen da suka riga ka gidan gaskiya, kamar yadda ɗan'uwanka, Haruna, ya rasu a Dutsen Hor, aka kai shi wurin mutanensa waɗanda suka riga shi gidan gaskiya.