Dukan taron jama'ar Isra'ila suka tashi daga jejin Sin, suna tafiya daga zango zuwa zango bisa ga umarnin Ubangiji. Suka yi zango a Refidim, amma ba ruwan da jama'a za su sha.
Taron jama'ar Isra'ila suka tashi daga Elim suka shiga jejin Sin wanda yake tsakanin Elim da Sina'i, a rana ta goma sha biyar ga watan biyu bayan fitowarsu daga ƙasar Masar.