Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 33:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Waɗannan su ne wuraren da Isra'ilawa suka yi zango sa'ad da suka fita runduna runduna daga ƙasar Masar ta hannun Musa da Haruna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Ga wuraren da Isra’ilawa suka yi sansani sa’ad da suka fito runduna-runduna a ƙarƙashin Musa da Haruna daga Masar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 33:1
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama na fito da ku daga ƙasar Masar, Na fanshe ku daga gidan bauta. Na aika muku da Musa, da Haruna, da Maryamu.


Ka bi da jama'arka yadda makiyayi yake yi, Musa da Haruna suke lura da su.


Sa'ad da Yakubu da 'ya'yansa suka tafi Masar, Masarawa suka wulakanta su, sai suka kai kuka ga Ubangiji. Ubangiji kuwa ya aiki Musa da Haruna waɗanda suka fito da kakanninku daga ƙasar Masar, suka kawo su su zauna a wannan wuri.


Na aiki Musa da Haruna, na aukar wa Masar da annobai ta wurin abin da na yi a cikinta daga baya kuma na fisshe ku.


Amma Allah ya kewaya da jama'a ta hanyar jeji, wajen Bahar Maliya. Isra'ilawa kuwa suka fita daga ƙasar Masar da shirin yaƙi.


A wannan rana ce Ubangiji ya fitar da Isra'ilawa runduna runduna daga ƙasar Masar.


Isra'ilawa mutum wajen zambar ɗari shida maza (600,000), banda iyalansu, suka kama tafiya daga Ramases zuwa Sukkot.


Bisa ga faɗar Ubangiji, Musa ya rubuta wuraren tashinsu da wuraren saukarsu. Wuraren saukarsu da na tashinsu ke nan.


Sai ya aiki bayinsa Musa da Haruna, waɗanda ya zaɓa.


Wannan Haruna ne da Musa, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana su fito da Isra'ilawa daga cikin ƙasar Masar, ƙungiya ƙungiya.


A ranar da shekara arbaminya da talatin ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan rundunar Ubangiji suka fita daga ƙasar Masar.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ