Daga Arower wadda take gefen kwarin kogin Arnon, zuwa Gileyad har ma da garin da yake cikin kwarin, Ubangiji Allahnmu ya ba da dukan kome a gare mu. Ba birnin da ya gagare mu.
Ya karkashe su da mummunan kisa tun daga Arower zuwa yankin Minnit, har zuwa Abel-keramim. Ya cinye biranensu guda ashirin. Da haka Ammonawa suka sha kāshi a hannun Isra'ilawa.