Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 32:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Kabilan Ra'ubainu da Gad suna da dabbobi da yawa ƙwarai. Da suka ga ƙasar Yazar da ta Gileyad wuri ne mai kyau domin shanu,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Mutanen Ruben da mutanen Gad, da suke da garken shanu da kuma garke tumaki masu yawa, suka ga cewa ƙasashen Yazer da Gileyad wurare ne masu kyau don kiwon shanu da tumaki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 32:1
30 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Musa ya aika a leƙo asirin ƙasar Yazar. Suka tafi suka ci ƙauyukanta, suka kori Amoriyawan da suke can.


suka ce, “Atarot, da Dibon, da Yazar, da Bet-nimra, da Heshbon, da Eleyale, da Simba, da Nebo, da Ba'al-meyon,


Don kuwa duk abin da yake duniya, kamar su sha'awa irin ta halin mutuntaka, da sha'awar ido, da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ne.


Sai ka yi kiwon mutanenka da sandanka, Wato garken mallakarka, Wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi A tsakiyar ƙasa mai albarka. Bari su yi kiwo cikin Bashan da Gileyad Kamar a kwanakin dā.


Zan komar da Isra'ila a makiyayarsa, zai yi kiwo a Karmel da Bashan. Zai sami biyan bukatarsa a tsaunukan Ifraimu da na Gileyad.


Suka haye Urdun suka fara daga Arower, da garin da yake tsakiyar kwarin zuwa Gad, har zuwa Yazar.


Yankin ƙasarsu shi ne Yazar, da dukan biranen Gileyad da rabin ƙasar Ammonawa zuwa Arower wadda take gabas da Rabba,


'Ya'yanmu, da matanmu, da tumakinmu, da shanunmu za su zauna a birane a nan Gileyad.


Babban taron tattarmuka kuma suka tafi tare da su, da garkunan tumaki da awaki, da na shanu tinjim.


Suka kuma ce wa Fir'auna, “Ranka ya daɗe, mun zo baƙunci ne cikin ƙasar, gama ba wurin kiwo domin garkunan bayinka, gama yunwa ta tsananta a ƙasar Kan'ana. Yanzu muna roƙonka, ka yarda wa bayinka su zauna a ƙasar Goshen.”


Lai'atu fa ta yi ciki ta haifi ɗa, ta raɗa masa suna Ra'ubainu, gama ta ce, “Saboda Ubangiji ya dubi wahalata, hakika, yanzu mijina zai ƙaunace ni.”


Lutu wanda ya tafi tare da Abram, shi kuma yana da garkunan tumaki, da na shanu, da alfarwai,


Yanzu Abram ya arzuta da dabbobi, da azurfa, da zinariya.


sai suka je wurin Musa da Ele'azara firist, da shugabannin taron jama'ar,


Zai zaɓar wa kansa wuri mai kyau, Gama wurin ne aka keɓe wa shugaba. Ya zo wurin shugabannin mutane, Tare da Isra'ila, ya aikata adalcin Ubangiji, Ya kiyaye farillansa.”


Sai Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka koma gida. Suka yi bankwana da sauran 'yan'uwansu Isra'ilawa a Shilo ta ƙasar Kan'ana. Suka koma ƙasar Gileyad, ƙasar da suka gāda bisa ga umarnin Ubangiji ta bakin Musa.


Don me suka tsaya daga baya tare da tumaki? Don su saurari makiyaya na kiran garkuna? Hakika kabilar Ra'ubainu ta rarrabu, Ba su shawarta su zo ba.


Abin da Ubangiji ya ce ke nan a kan fādar Sarkin Yahuza, “Kyanta kamar Gileyad take a gare ni, Kamar kuma ƙwanƙolin Lebanon. Duk da haka zan maishe ta hamada, Birnin da ba kowa ciki.


Mutanen Isra'ila kuwa suka aiki Finehas, ɗan Ele'azara, firist, wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad.


Sa'an nan suka zo Gileyad da Kadesh cikin ƙasar Hittiyawa, daga nan suka tafi Dan-ja'an. Daga Dan-ja'an kuma suka ratsa zuwa Sidon.


Waɗannan da aka lasafta sunayensu, su ne suka zo a kwanakin Hezekiya Sarkin Yahuza, suka fāɗa wa alfarwai da bukkoki waɗanda suka tarar a can, suka hallaka su sarai, sa'an nan suka maye wurinsu saboda akwai makiyaya domin garkunansu a wurin.


Ba abin sanyayawa a Gileyad ne? Ba mai magani a can ne? Me ya sa ba a warkar da jama'ata ba?


Zan yi kuka saboda kurangar inabin Sibma Fiye da yadda zan yi kuka saboda mutanen Yazar. Rassanku sun haye teku har sun kai Yazar, Amma mai hallakarwa ya faɗo a kan 'ya'yan itatuwanku da damuna Da kan amfanin inabinku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ