Jonatan ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye zuwa sansanin marasa kaciyan nan, arnan nan, watakila Ubangiji zai yi aiki ta wurinmu, gama ba abin da zai hana Ubangiji ya yiwo ceto ta wurin masu yawa, ko kuwa ta wurin 'yan kaɗan.”
Ubangiji kuwa ya ce wa Gidiyon, “Mutanen da suke tare da kai sun yi yawa da zan ba da Madayanawa a hannunsu, kada ya zama Isra'ilawa su yi mini fāriya, su ce, ‘Ƙarfinmu ne ya cece mu.’
Musa kuwa ya ce wa jama'a, “Ku sa mazajen da suke cikinku su yi shiri, su yi ɗamarar yaƙi, don su tafi su yi yaƙi da Madayanawa, su ɗaukar wa ubangiji fansa a kansu.