Amma mata, da yara, da dabbobi, da dukan abin da yake cikin garin, da dukan ganimarsa, sai ku kwashe su ganima, ku mori ganimar magabtanku, wadda Ubangiji Allahnku ya ba ku.
Za ka yi wa Ai da sarkinta kamar yadda ka yi wa Yariko da sarkinta, sai dai ganima da dabbobinta ne za ku washe domin kanku. Ku yi kwanto a bayan birnin.”
Isra'ilawa kuma suka kwashe ganima ta abubuwa masu tamani na biranen game da shanu, amma suka kashe kowane mutum da takobi, har suka hallakar da su, ba su bar kowa ba.