Saboda haka, bala'inta zai aukar mata rana ɗaya, Mutuwa, da baƙin ciki, da yunwa. Za a kuma ƙone ta, Domin Ubangiji Allah da yake hukunta ta Mai Ƙarfi ne.”
Gama Fir'auna ya haura, ya ci Gezer, ya ƙone ta da wuta, ya kuma kashe masu zama cikinta. Sa'an nan ya yi wa 'yarsa, wato matar Sulemanu, kyauta da Gezer ɗin.
Sa'ad da Dawuda da mutanensa suka koma Ziklag a rana ta uku, sai suka tarar Amalekawa sun riga sun kawo wa Negeb da Ziklag hari. Suka cinye Ziklag, suka ƙone ta.
Suka ƙone birnin da wuta da dukan abin da yake a cikinsa, sai dai azurfa, da zinariya, da kwanonin tagulla, da na baƙin ƙarfe ne, suka ajiye a cikin taskar masujadar Ubangiji.