Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 3:50 - Littafi Mai Tsarki

50 Kuɗin da ya karɓa daga 'ya'yan fari na Isra'ilawa da suka haura yawan Lawiyawa shekel dubu ɗaya da ɗari uku da sittin da biyar (1,365) bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

50 Daga ’ya’yan fari na Isra’ilawa, ya karɓi azurfa masu nauyin shekel 1,365, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 3:50
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah. An kashe shi a jiki, amma an rayar da shi a ruhu.


Domin kun sani an fanshe ku ne daga al'adunku na banza da wofi da kuka gāda, ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa da zinariya ba,


Almasihu ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak, ba ƙari, ba kuwa ta wurin jinin awaki ko na 'yan maruƙa ya shiga ba, sai dai ta wurin nasa jini, ya samo mana madawwamiyar fansa.


wanda ya ba da kansa dominmu, domin ya fanso mu daga dukan mugun aiki, ya kuma tsarkake jama'a su zama abin mulkinsa, masu himmar yin kyakkyawan aiki.


kamar yadda Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba sai dai domin shi ya yi bautar, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”


Musa kuwa ya karɓi kuɗin fansar waɗanda suka haura yawan Lawiyawa.


Musa kuwa ya ba Haruna da 'ya'yansa maza kuɗin fansa bisa ga maganar Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ