Amma Nadab da Abihu sun mutu a gaban Ubangiji a jejin Sinai, a sa'ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta. Sun mutu, ba su da 'ya'ya, saboda haka Ele'azara da Itamar suka yi aikin firist su kaɗai a zamanin mahaifinsu Haruna.
Lawiyawa kuma ba za su rasa firistocin da za su tsaya a gabana, suna miƙa hadayun ƙonawa ba, da hadayu na gari na ƙonawa, su kuma miƙa sadaka har abada.”
Za su zama masu hidima a cikin wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin Haikali, suna hidima a cikin Haikalin. Za su yanka hadayar ƙonawa da ta sadaka domin mutane. Za su lura da mutanen, su yi musu hidima.