48 Sai ka ba da kuɗin fansar ga Haruna da 'ya'yansa maza.”
48 Ka ba wa Haruna da ’ya’yansa kuɗin fansar da ya haura kai na ’ya’yan farin Isra’ilawa.”
Ka karɓi shekel biyar a kan kowane mutum, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.
Musa kuwa ya karɓi kuɗin fansar waɗanda suka haura yawan Lawiyawa.
Musa kuwa ya ba Haruna da 'ya'yansa maza kuɗin fansa bisa ga maganar Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.