Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 3:41 - Littafi Mai Tsarki

41 Za ka keɓe mini Lawiyawa a maimakon 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa. Dabbobin Lawiyawa za su zama nawa a maimakon dukan 'ya'yan farin dabbobin Isra'ilawa. Ni ne Ubangiji.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

41 Ka ɗauko mini Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari na Isra’ilawa, haka ma na dabbobi na Lawiyawa, a maimakon ’ya’yan fari na dabbobin Isra’ilawa. Ni ne Ubangiji.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 3:41
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ga shi, na ɗauki Lawiyawa daga cikin Isra'ilawa a maimakon kowane ɗan farin da ya buɗe mahaifa daga cikin mutanen Isra'ila. Lawiyawa za su zama nawa.


“Ka keɓe Lawiyawa a maimakon dukan 'ya'yan fari na Isra'ilawa. Dabbobin Lawiyawa kuma za su zama a maimakon 'ya'yan farin dabbobin Isra'ilawa. Lawiyawa kuwa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.


wanda ya ba da kansa fansa saboda kowa da kowa. An kuwa yi shaidar wannan a daidai lokacinsa.


kamar yadda Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba sai dai domin shi ya yi bautar, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”


“Dukan haihuwar fari, ko ta mutum ko ta dabba da sukan bayar ga Ubangiji zai zama naka. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram.


Gama dukansu an ba ni su daga cikin Isra'ilawa a maimakon dukan waɗanda suka fara buɗe mahaifa, wato dukan 'ya'yan farin Isra'ilawa. Na karɓi Lawiyawa su zama nawa.


Sai Musa ya ƙidaya 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.


Gama 'yan fari duka nawa ne, tun daga ranar da na kashe 'ya'yan fari na ƙasar Masar, na keɓe wa kaina duk ɗan fari na Isra'ila, na mutum da na dabba. Za su zama nawa, ni ne Ubangiji.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ